Sojojin Yemen sun kai hari kan sansanin Nevatim na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke Negev da makami mai linzami
Dakarun Yemen sun sanar da aiwatar da wani farmakin soji kan sansanin sojojin saman Nevatim na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Negev a kudancin Falasdinu da aka mamaye.
Rundunar sojin kasar Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar cewa: Rundunarta ta kai wani harin soji kan sansanin sojin saman Nevatim da ke yankin Negev da makami mai linzami na kirar “Falestine 2”.
Majiyar ta kara da cewa: Makami mai linzamin ya kai ga inda aka saita, kuma na’urorin kariya na haramtacciyar kasar Isra’ila sun kasa kakkaboshi. Ta yi nuni da cewa: Wannan farmakin wata nasara ce ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da mayakansu, da kuma yin watsi da kisan kiyashin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi kan ‘yan uwan al’ummar Yemen a Zirin Gaza.