Sojojin Yemen Sun Kai Hare Hare Kan Birnin Eilat Ko Ummu RashRash Na Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye

Kakakin sojojin kasar Yemen Burgedia Janar Yahyah Saree ya bayyana cewa sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami samfurin Bailistic kan birin Ummu Rasha Rash

Kakakin sojojin kasar Yemen Burgedia Janar Yahyah Saree ya bayyana cewa sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami samfurin Bailistic kan birin Ummu Rasha Rash (eilat) na kasar Falasdinu da aka mamaye kuma makaman sun sami bararsu kamar yadda a aka tsara.

Banda haka labarin ya kara da cewa sojojin kasar ta Yemmen sun cilla makamai masu linzami da kuma jiragen yaki masu kunan bakin wake kan wani jirgin yakin kasar Amurka dake cikin tekun Maliya wanda ake kira ‘Pumba’ kuma makaman sun sami jirgin kamar yadda ake so.

Daga karshe Yahyah Saree ya kara da cewa, hare haren kasashe Amurka, Burtania da kuma HKI a kan kasar Yemen ba za su taba sa kasar ta jenaye daga matakan da ta dauka na tallafawa Falasdinawa wadanda aka zalunta ba.

Ya zuwa yanzu dai kasar Yemen ta sami nasara a matakan da ta dauka na hana jiragen ruwa masu zuwa HKI wucewa ta tekun Maliya ko babul Mandab. Gwamnatocin kasashen Amurka da Burtania sun kafa kawancen kasashe a tekun Red sea ko (Malia) don hana kasar Yemen ci gaba da hana jiragen HKI ko wadanda suke zuwa kasar wucewa, amma sun kasa yin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments