Bayan harin wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya suka kai wa Yemen, sojojin kasar sun harba makamai masu linzami kan birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar Isra’ila
Kasashen Amurka da Birtaniya sun kai wasu hare-haren wuce gona da iri ta sama kan lardin Hodeidah dake gabar tekun kasar Yemen, a kokarin hana sojojin Yemen kai hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila, inda bayan nan sojojin kasar ta Yemen suka kai hare-hare da makamai masu linzami kan birnin Tel Aviv fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da wasu yankuna.
Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sar’e ya bayyana cewa: Jiragen yakin Amurka da na Birtaniya sun kai farmaki ta sama a yammacin jiya Litinin kan gundumar Al-Tuhayta da ke kudancin lardin Hodeida, inda daga bisani sojojin Yemen suka kaddamar da hare-hare da makamai masu linzami kan birnin Tel Aviv da wasu yankuna na haramtacciyar kasar Isra’ila.
Bayan wani dan lokaci kadan da kai hare-haren Yemen kan tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila, sai aka kunna karar gargadi kan yahudawan sahayoniyya su shige maboyar karkashin kasa a Urushalima da Tel Aviv tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na Ben Gurion.