Jiniyoyin gargadi sun tashi a birnin Tel’aviv na HKI a safiyar yau litinin bayan da sojojin kasar Yemen suka cilla makami mai linzami samfurin bilistic a kan birnin.
Tashar talabijin ta Al-Alam mai watsa shirye-shiryensa da harshen larabaci a nan Tehran ta ce, makamin mai linzami safurin bilistic ya fada kan birnin ya kuma sa aka rufe tashar Jiragen sama ta Bengerion, aka hana sauka da tashin jiragen sama.
Kafafen yada labarai na HKI sun bayyana cewa miliyoyin mutane a birnin sun yi sauri sun shiga wuraren da aka tanadar don samun mafaka daga faduwar makaman makiya a kansu. Labarin ya kara da cewa wasu da dama sun ji rauni a lokacin da suke gudu don samun mafaka a wuraren da aka tanadar don hakan.
Kafafen yada labaran basu bayyana irin barnan da makamin ya yi ba ko kuma asarar da ya jawo a birnin.