Sojojin Yemen Ne Suka Tilastawa Amurka Dakatar Da Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Kasarsu

Wani babban hafsan sojin Yemen ya bayyana dabarun Yemen da suka tilastawa Amurka dakatar da kai hare-hare kan kasar Yemen Kwararren kan harkar sojin kasar

Wani babban hafsan sojin Yemen ya bayyana dabarun Yemen da suka tilastawa Amurka dakatar da kai hare-hare kan kasar Yemen

Kwararren kan harkar sojin kasar Yemen kuma kwararre kan harkar yaki Birgediya Janar Aziz Rashid ya jaddada bunkasar karfin sojan kasar Yemen, yana mai nuni da dalilan da suka sanya aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Yemen.

A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, kwararren sojan kasar Yemen kuma kwararre kan harkar dabarun yaki birgediya Janar Aziz Rashid ya tabbatar da cewa: Kasar Yemen ta samu wani matsayi mai inganci a arangamar da take yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta yi nasarar sauya ma’aunin karfin iko da kuma karuwar matakan soji da sabbin ka’idojin arangama kan makiya.

Birgediya Janar Rashid ya yi nuni da cewa dakarun kasar Yemen sun tilastawa Amurka gaggauta kawo karshen ta’asarta ta hanyar tuntubar mai shiga tsakani na kasa da kasa na kasar Oman. An dai cimma matsaya kan kauracewa luguden wuta kan kasar Yemen, domin kauracewa kai hari kan jiragen ruwan Amurka, muddin Amurka ta kuduri aniyar kawo karshen kai hari kan Yemen.

Ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wutar ta zo ne bayan faduwar jiragen saman Amurka guda uku samfurin F-18. Sun danganta faduwar jirgin na farko da harbin abokan Amurka, na biyu kuma da juyowar da jirgin dakon jiragen saman Amurka ya yi da kuma yin artabu da sojojin Yemen daga baya. Dangane da na uku kuma, sun kasa yin karya game da musabbabin faduwar jirgin, lamarin da ya sa Trump ya tuntubi mai shiga tsakani na Amurka don gaggauta tsagaita bude wutar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments