Falasdinawa sun yi shahada yayin da wasu suka samu raunuka sakamakon hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan biranan Khan Yunis da Jabaliya
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Wafa cewa: Wasu Falasdinu da dama sun yi shahada, wasu kuma suka jikkata, kafin wayewar garin yau Alhamis, sakamakon ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan sassa daban-daban na Zirin Gaza.
Rahoton ya bayyana cewa: An gano gawar wasu shahidai biyu da wasu da dama da suka samu raunuka, sakamakon luguden wuta da jirgin saman yakin yahudawan sahayoniyya ya kai kan gidan iyalan Kalab da ke tsakiyar birnin Khan Yunis a kudancin Zirin Gaza.
Har ila yau jirgin saman sojin mamayar ya kai harin kan wani gida da ke yankin hukumar kwastam da ke gabashin birnin Khan Yunus, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuka da jikkatar wasu Falasdinawa a cewar majiyoyin lafiya, baya ga wasu mutane da suka bace a karkashin baraguzan gine-gine.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 ne sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suke ci gaba da kai hare-hare kan zirin Gaza ta kasa da ruwa da kuma ta sama, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 41,495 tare da jikkata wasu 96,006 wadanda yawancinsu yara da mata ne, yayin da dubban mutane suka bace da suka kasance a ƙarƙashin baraguzan gine-gine.