Search
Close this search box.

Sojojin Yahudawan Sahayoniyya Sun Yi Luguden Bama-Bamai Kan Sansanin Falasdinawa Na Nuseirat

Sojojin yahudawan sahayoniyya sun yi luguden bama-bamai kan sansanin Falasdinawa na Nuseirat lamarin da ya janyo shahadar Falasdinawa bakwai Wasu Falasdinawa bakwai sun yi shahada,

Sojojin yahudawan sahayoniyya sun yi luguden bama-bamai kan sansanin Falasdinawa na Nuseirat lamarin da ya janyo shahadar Falasdinawa bakwai

Wasu Falasdinawa bakwai sun yi shahada, yayin wasu suka jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Zirin Gaza a safiyar yau Talata.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa: Jirgin saman yakin gwamnatin mamayar yahudawan sahayoniyya ya kaddamar da wasu hare-hare a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar Falasdinawa bakwai tare da jikkata wasu na daban.

Haka nan jirgin saman yakin gwamnatin mamayar ya yi ruwan bama-bamai a yankuna da dama na tsakiyar yankin Zirin Gaza, musamman birnin Deir al-Balah da kuma sansanin Bureij.

Har ila yau sojojin mamayar sun kai hari kan yankunan da suke yammacin birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne, sojojin mamaya suke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza ta kasa da ruwa da kuma ta sama, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 37,347, wadanda akasarinsu mata da kananan yara ne, da kuma jikkata wasu 85,372 na daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments