Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun afkawa Qalqilya da Tulkaram tare da raunata wani bature mai fafutuka a Nablus
Da sanyin safiyar yau Asabar ne sojojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai farmaki a garuruwan Qalqilya da Tulkaram da ke yankin yammacin gabar kogin Jordan da ke arewacin Falasdinu, yayin da wani dan fafutuka dan kasar waje ya samu raunuka sakamakon harbinsa da sojojin mamaya suka yi a garin Nablus.
Wakilin gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa: Wani Bafalasdine ya samu rauni a lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kutsa cikin birnin Qalqilya daga mashigar gabashin Falasdinu, kuma majiyoyin cikin gida sun ce sojojin mamayar sun harba harsashi mai rai a yayin harin, wanda ya yi sanadin jikkatar mutum guda.
Sojojin mamaya sun kuma kai samame a wasu unguwanni a cikin birnin, lamarin da ya janyo bullar arangama da matasan Falasdinawa kafin sojojin su fice daga birnin.