Sojojin Syria Sun Sake Kwato Da Rundunar Soja Ta 87 Da Kuma Filin Jirgin Sama Na  Humah

Da marecen jiya Alhamis ne dai sojojin na Syria su ka sanar da sake zubin jan dagar da su ka yi a tsakiyar Humah domin

Da marecen jiya Alhamis ne dai sojojin na Syria su ka sanar da sake zubin jan dagar da su ka yi a tsakiyar Humah domin kare rayukan fararen hula bayan harin da masu dauke da makamai su ka kai a cikin garin.

Tun da fari ministan tsaron kasar ta Syria Imad Ali Mahmud Abbas  wanda ya yi jawabi ta kafar talbijin din kasar Syria ya bayyana cewa; A wasu lokutan dubarun yaki suna da bukatar a sauya zubin jan daga, da inda aka girke sojoji.

Ministan tsaron na Syria ya kuma kara cewa; Kasar Syri da sojojinta da al’ummarta da kuma taimakon kawayenta za su iya samun nasara su tsallake wannan kalubalen da ake fuskanta.

Bugu da kari, ministan na tsaron kasar Syria ya zargi masu dauke da makaman da haddasa hargitsi a cikin kasar. Haka nan kuma yadda kungiyoyin suke fitar da bayanai da bayar da umarni na bogi da sunan jami’an tsaron kasar ko kuma rundunar soja.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments