Sojojin Sudan Sun Kwace Wuri Na Karshe Da Yake A Hannun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” A Cikin Birnin Khartum

Rundunar sojan Sudan ta sanar da shimfida ikonta akan filin saukar jiragen sama na Khartum wanda shi ne tunga ta karshe da ta saura a

Rundunar sojan Sudan ta sanar da shimfida ikonta akan filin saukar jiragen sama na Khartum wanda shi ne tunga ta karshe da ta saura a hannun rundunar kai daukin gaggawa.

Kwamandan rundunar sojan Sudan da take fada a birnin na Khartum Lafatnar kanar Abdurrahman al-Bilawi ne ya sanar da cewa, an  shimfida iko a  cikn filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na birnin Khartum.

Har ila yau yau kwamandan sojan ya kuma bayyana cewa, a yanzu haka suna cigaba da faraurar mayakin “Rundunar Kai Daukin Gaggawa”da su ka saura a cikin binin Khartum.

Tun da safiyar yau Laraba ne dai sojojin na Sudan suka sanar da cewa suna samun Karin nasara akan abokan fadansu.

Wata majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labaurn Faransa cewa; sojojin Sudan din sun killace  yankin Jabalu-Auliya, dake kudancin Khartum, da kuma hanyoyin da su ka nufi kusurwowin arewa, kudu da gabas.

Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai sojojin na Sudan su ka kwato fadar shugaban kasa wacce ta dauki shekaru biyu a hannun rundunar kai daukin gaggawa, haka nan kuma babbar cibiyar soja da tsakiyar birnin Khartum da can ne ma’aikatu da dama suke.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments