Sojojin Sudan Sun Kwace Iko Da Birnin Wad Madani Fadar mulkin Jihar Aljazira Na Kasar

Sojojin Sudan sun sake kwace iko da birnin “Wad Madani”, fadar mulkin jihar Aljazira daga mayakan Dakarun kai daukin gaggawa Bayan shekara guda da Dakarun

Sojojin Sudan sun sake kwace iko da birnin “Wad Madani”, fadar mulkin jihar Aljazira daga mayakan Dakarun kai daukin gaggawa

Bayan shekara guda da Dakarun kai dauki gaggawa na Rapid Support Forces suka kwace iko da birnin Wa Madani fadar mulkin jihar Aljazira, sojojin Sudan sun samu nararar murkushe dakarun kai daukin gaggawan tare da karbe iko da madafun shugabancin birnin na Wad Madani.

Rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa: Sojojinta sun samu nasarar mamaye birnin Wad Madani, kuma wasu dakaru masu dauke da makamai da suke goyon bayan sojojin kasar suna ci gaba kutsawa kowane yankin birnin domin tsarkakeshi daga samuwar mayakan dakarun kai daukin gaggawa. Kamar yadda rundunar sojin ta tsaurara matakan tsaro, tare da ci gaba da kai hare-hare kan duk wani wuri da ake tsammanin samuwar Dakarun kai daukin gaggawa a cikin birnin, yayin da rahotonni suka bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa sun tsere daga birnin zuwa Hasahisa da Al-Kamlin.

Sojojin sun tabbatar da cewa: Suna da niyyar ci gaba da yakar Dakarun kai daukin gaggawan har sai sun kai ga ‘yantar dukkanin yankunan jihar Aljazira da kuma ‘yantar da kasar Sudan baki daya, kamar yadda suka bayyana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments