Sojojin Sudan Sun Kwace Iko Da Birnin Al-Dindar Da Ke Hannu Dakarun Kai Dauki Gaggawa

Sojojin Sudan sun kwace iko da birnin Al-Dindar da ke karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa Majiyoyin watsa labaran Sudan sun shaidawa gidan talabijin na

Sojojin Sudan sun kwace iko da birnin Al-Dindar da ke karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa

Majiyoyin watsa labaran Sudan sun shaidawa gidan talabijin na Al Jazeera Net cewa: Sojojin Sudan sun yi galaba a kan mayakan dakarun kaidaukin gaggawa na Rapid Support Forces a yammacin jiya Laraba, inda suka kwace iko da birnin Dinder na jihar Sinnar bayan kazamin fada da aka gwabza, tare da karfafa ikonsu a birnin.

Ana ɗaukar birnin Dinder a matsayin yanki mai mahimmanci ta fuskar soja, saboda akwai gada daya tilo a kan kogin Dinder da ake amfani da shi a mafi yawanci yankin.

Samun nasarar kwace iko da birnin Dinder zai sanya sojoji da ke gabashin kogin Dinder su samu damar tafiya cikin walwala zuwa birnin Sinja fadar mulkin jihar Sinnar, da sauran yankunan da suke kusa da yankunan da suke karkashin ikon Dakarun kaidaukin gaggawana Rapid Support Forces.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments