Babban birnin kasar Sudan, Khartoum, shi ne tushen rikicin kasar da a halin yanzu aka shafe makonni ana gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan dakarun kai daukin gaggawa, amma fadan ya kara kamari a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Sojoji suna kara ci gaba da tunkarar babban birnin kasar bayan fitattun sojojin kasar da suka hada da sojoji da mayaka masu goyon bayan sojoji da hukumar leken asiri da dakarun tsaron Sudan da suke sansanin Haddab da ke bangaren arewa maso gabashin yankin Gabashin Nilu a arewa maso gabashin Khartoum suka doshi birnin na Khartoum da nufin ‘yantar da shi gaba daya daga hannun mayakan dakarun kaidfaukin gaggawa.
Wata majiyar sojan ta bayyana cewa: Sojoji da dakarun da ke mara musu baya sun tunkari hedikwatar bataliya ta dabarun yaki a yankin Maqran Al-Nilu biyu a birnin Khartoum.