Sojojin Sudan Da Dakarun Kai Daukin Gaggawa Suna Gwabza Fada A Arewacin Birnin El Fasher

Ana gwabza mummunan fada tsakanin sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawa a shiyar arewacin birnin El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa Majiyoyin

Ana gwabza mummunan fada tsakanin sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawa a shiyar arewacin birnin El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa

Majiyoyin da ke da alaka da ƙungiyoyi masu dauke da makamai da suke kawance da sojojin Sudan sun shaida wa tashar talabijin ta Aljazeera cewa: Mayakansu suna ci gaba da gwabza kazamin fada da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces a yankin Zarq na arewacin Darfur.

Haka nan, majiyar ta tabbatar da cewa: Ana ci gaba da gwabza fada a kusa da yanki mai tazarar kilomita 120 daga arewacin birnin El Fasher, fadar mulkin jihar El-Fasher, kuma wannan yanki da ke cikin sahara na matsayin wani muhimmin sansanin na musamman na samar da kayan aiki ga dakarun kai daukin gaggawa na rapid support forces.

Majiyar rundunar sojin Sudan ta kuma bayyana cewa: Sojojinta sun yi wa dakarun kai daukin gaggawar mummunar hasarar rayuka da kayayyakin aiki, inda suka yi nasarar kawar da wasu da dama daga cikin makaman kare kai na dakarun kaidaukin gaggawa na Rapid Support Forces a yankin Jabra da ke kudancin birnin Khartoum.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments