Sojojin ‘yan Sahayoniyya suna ci gaba da gudanar da kisan kiyashi a Gaza, bayan shahadan Falasdinawa 33 sakamakon hari kan wasu gidaje a sansanin Jabaliya
Gidan talabijin na Aljazeera ya watsa rahoton cewa: Falasdinawa 33 ne suka yi shahada wasu fiye da 70 kuma suka jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin gwamnatin ‘yan sahayoiniyya suka kai kan wasu gidaje a mahadar Nassar da ke sansanin Jabaliya da yammacin jiya Juma’a.
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya ce daga cikin wadanda suka yi shahada har da mata 21.
Wakilin gidan talabijin na Aljazeera ya kuma tabbatar da cewa: Adadin Falasdinawan da suka yi shahadan a hare-haren bama-baman da aka kai garin Tal al-Zaatar da ke arewacin Gaza ya kai shahidai 30 da suka hada da yara da mata 20, baya ga shahidai biyu da jikkatan wasu da dama a harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wani gida da ke cikin Sansanin Maghazi a tsakiyar Zirin Gaza.
Wannan adadin dai ya kawo adadin shahidai sakamakon hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a zirin Gaza tun daga wayewar garin ranar Juma’a zuwa shahidai 64 ciki har da 45 a sansanin Jabaliya.