A wani labari da kungiyar “ISWAP” mai alaka da “Isis” ta watsa, ta sanar da kashe wani babban jami’in sojan Najeriya a wani kwanton bauna da ta yi wa sojoji a kusa da kauyen Wajiroko dake Jahar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata.
Sanarwar kungiyar ta “Isis” ya kuma kunshi cewa, baya ga Birgediya janar Uba da su ka kashe, sun kuma kashe wasu sojojin 4.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” da ya tuntubi rundunar sojan kasar ta Najeriya domin samun Karin bayani akan abinda ya faru bai sami jawabi ba.
Sai dai rundunar sojan ta Najeriya ta ce labarin da ake watsawa na kama babban jami’i mai mukamin Birgediya janar, ba gaskiya ba ne, kuma bai kamata ‘yan kasa su gaskata shi ba.
Mayakan kungiyar ta “Iswap” sun buga a shafinsu mai suna “A’amaq” cewa, sun kashe jami’in sojan, a wani kwanton bauna da su ka yi .
Jahar Borno tana fada da matsalar masu dauke da makamai da suke ikirarin jihadi, tun daga 2009, wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan dubban mutane da kuma mayar da wasu zama ‘yan hijira nesa da gidajensu.
Ita dai kungiyar “Iswap” ta balle daga Bokoharam, bayan da su ka sami sabani, da a karshe ya kai ga kashe magudun kungiyar Abubakar Shekau.