Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane

Majiyar hatkwatan sojojin Najeriya ta musanta labaran da suke yaduwa kan cewa, an fasa gudanar da faretin cika shekaru 65 da samun yencin kan kasar

Majiyar hatkwatan sojojin Najeriya ta musanta labaran da suke yaduwa kan cewa, an fasa gudanar da faretin cika shekaru 65 da samun yencin kan kasar a ranar daya ga watan Octoba ne saboda yunkurin yi wa  shugaba Bola Ahmad Tunubu juyin mulki ne.

Jaridar daily Trust ta Najeriya ta nakalto majiyar sojojin kasar na musanta aukuwar haka, kuma tace labarin jita-jita ne wanda bai da kanshin gaskiya a cikinsa. Babu wani kokarin juyin mulki a kasar, inji majiyar.

Sojojin sun ce an fasa gudanar da faretin cika shekaru 65 da samun yencin kan kasar ne, saboda bawa shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu damar halattan wasu tarurruka masu muhimmanci a kasashen waje, kuma fasawar bai da dangantaka ko kadan da juyin mulki.

Daily trust ta nakalto darakta mai kula da al-amuran yada labaran tsaron kasa,  Brigadier General Tukur Gusau yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma yi kira ga yan kasa su yi wati da labarin su kuma ci gaba da harkokinsu, yace sannan makiyan Najeriya ne suke yada wannan labarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments