Jami’in sojan Masar sun bayyana cewa: A shirye suke su kalubalanci duk wata barazana daga haramtacciyar kasar Isra’ila
Shugaban Kwamitin Tsaro da Tsaron al’umma a Majalisar Wakilan kasar Masar, Manjo Janar Ahmed Al-Awadi, ya ce: Sojojin Masar na can a yankin Sinai a yankunan da suke kan iyaka da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Da yake mayar da martani ga wata tambaya: Shin sojojin Masar sun sake tura sojojinsu zuwa yankunan da aka haramta musu shiga bisa yarjejeniyar zaman lafiya, Al-Awadi ya bayyana a yayin ganawarsa da jaridar Newsmaker cewa, sojojin Masar na girke a dukkan yankuna da kuma kan iyakar Masar da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya ci gaba da cewa: Bisa la’akari da wannan yanayi mai zafi a kan iyakokin Masar da haramtacciyar kasar Isra’ila, bai dace ba a ce sojojin Masar za su tsaya su jira har sai “Isra’ila” ta ba ta mamaki bisa hujjar yarjejeniyar zaman lafiya, yana mai cewa: akwai kan iyaka sasanniya da tsallake ta ke matsayin karya wannan yarjejeniya, amma sojojin Masar ba za su tsaya su zuba ido saboda akwai kan iyaka da aka shata ba har sai al’amura sun tabarbare.