Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da rusa ababen more rayuwa a birnin Tul-karam da sansanoninsa na Falasdinu tare da kama Falasdinawa da tilasta wa jama’a yin gudun hijira
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tul-Karam da sansanoninsa guda biyu Tul-karam da Nourul- Shams a rana ta 16 a jere, a daidai lokacin da sojoji ke ci gaba da barnata kayayyakin more rayuwa da kadarorin jama’a da kuma kame jama’a gami da tilastawa dubban mazauna sansanonin biyu gudun hijira.
Sojojin mamayar suna ci gaba da killace sansanonin Tulkaram da Nourul Shams, sannan kuma suna kara yawan sintirin motocinsu da na tankokin yakinsu da kuma sintiri da kafa a yankuna da unguwannin su, a daidai lokacin da ake kai hare-hare kan gidajen Falasdinawa, inda da yawansu suka zama babu kowa a ciki, bayan ga tilastawa mazauna su kauracewa gidajensu, inda ake yi ta harbe-harbe da muggan makamai, musamman da daddare kan gidajen.