A hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila kai kan yankunan Zirin Gaza a cikin dare daya sun kashe Falasdinawa 51
Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai kan arewaci da kudancin zirin Gaza tun daga tsakiyar daren Laraba ya kai Falasdinawa 51, ciki har da 45 a arewacin zirin Gaza. Wannan sabon tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke gudanar da ziyarar aiki a yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinawan “WAFA” ya watsa rahoton cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudanci da arewacin zirin Gaza ya kai 51 tun da tsakar daren jiya, ciki har da shahidai 45 a arewacin zirin Gaza.
Wannan kisan kiyashi na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila, da kuma kasancewar shugaban Amurka Donald Trump a halin yanzu a yankin Gabas ta Tsakiya, inda yake cewa: Al’ummar Falasdinu a Gaza sun cancanci kyakkyawar makoma.