Da kadan-kadan, hare-haren yahudawan sahayoniyya sun kai kan fadar shugaban kasar Siriya da kuma babban hafsan sojin kasar
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai wasu jerin hare-hare ta sama kan hedikwatar Janar din da ke birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya a yau Laraba.
Wata majiyar Siriya ta tabbatar da cewa; Hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai ta sama sun janyo barna masu yawa a ginin Hafsan Sojin, majiyar ta kuma kara da cewa; Hare-haren bama-baman na Isra’ila sun auna fadar shugaban kasa ta “Fadar Tishreen”, ba fadar jama’a ba.
Majiyar ta kuma watsa rahoton cewa: Mahukuntan kasar ta Siriya sun fara kwashe nasu ya nasu daga babban ofishin gidan rediyo da talabijin na kasar.
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta kasar Siriya ta sanar da cewa: Jiragen saman yakin gwaamnatin mamayar Isra’ila sun kai hare-hare kan wasu motocin sojojin gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Siriya a birnin Sweida da kewaye, a wani sabon ci gaba da aka samu a kasa a kudancin kasar ta Siriya.