Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon  

Mutum guda ya yi shahada wasu uku kuma suka jikkata a harin da Yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankin kudancin Lebanon An kashe mutum guda,

Mutum guda ya yi shahada wasu uku kuma suka jikkata a harin da Yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankin kudancin Lebanon

An kashe mutum guda, wasu uku kuma sun ji rauni a hare-haren jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suka kai kan garin Tura da ke gundumar Taya na kasar Lebanon, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiyar Jama’a ta Lebanon ta fitar.

Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Ma’aikatar Lafiyar Jama’a ta sanar a cikin wata sanarwa cewa: “Harin jiragen saman gwamnatin mamayar Isra’ila a kan garin Tura da ke gundumar Taya a yankin kudancin Lebanon ya haifar da mutuwar mutum ɗaya, wasu uku kuma sun ji rauni.”

A wani hari na daban, wani jirgin saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila ya jefa bam mai ban tsoro a yankin Ras al-Naqoura.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted