Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula, inda suka kashe mutane 5 da suka hada da yara 3 a kudancin kasar Lebanon
Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da mutuwar wasu ‘yan kasar 5 da suka hada da yara uku sakamakon wani hari da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudancin birnin Bint Jabeil.
Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon ya watsa rahoton cewa: Wani jirgin sama mara matuki na makiya yahudawan sahayoniyya ya kai hari kan wani babur da wata mota dauke da makamai masu linzami a garin Bint Jabeil, lamarin da ya yi sanadin mutuwa da jikkata.
Wannan harin wuce gona da iri ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da keta hurumin kasar Labanon da kuma kai hare-hare kan fararen hula, wanda ya zo daidai da taron kwamitin membobi biyar a Naqoura, domin tattauna batun tsagaita wuta.
A cikin wannan yanayi, majiyoyin yada labarai na kasar Labanon sun ruwaito cewa: Wasu jiragen yaki mara matuki guda uku dauke da makamai sun yi shawagi da sanyin safiyar yau a kan birnin Bint Jabeil.