Kakakin sojan HKI ya sanar da cewa; An kashe sojoji 5 na rundunar Gulani a kudancin Lebanon a jiya Laraba daga cikinsu da akwai kwamanda na ayari na 51 a karkashin babbar rundunar Gulani.
Majiyar sojojin mamayar ta kara da cewa; arayin na soja sun shiga cikin wani gini ne a kudancin Lebanon, inda su ka fuskanci bude wuta daga kurkusa.
Shi kuwa Rediyon sojan HKI ya ce, sojojin sun fuskanci bude wuta ne daga mayakan Hizbullah 4 da su ka fito daga wani rami. Bugu da kari, wasu mayakan na Hizbullah da suke a cikin wani gini da yake kusa, sun yi kwanton bauna inda su ka bude wuta akan sojojin na mamaya da suke cikin daya ginin.
Bayan kawo karshen fadan wanda ya fara tun daga karfe;10;00 na safe har zuwa karfe 6;00 na yamma, sojojin mamayar sun iya dauke gawawwakin abokansu a karkashin bude wuta mai tsanani daga mayakan Hizbullah,kamar yadda Radiyon na soja ya bayyana.