Sojojin Kasar Yemen Sun Harbo Makamimai Masu Linzami Kan HKI A Daren Jiya

Sojojin kasar Yemen sun bada labarin cilla wasu karin makamai masu linzami kan HKI a tsiyar daren jiya, wanda yasa jiniyoyin girgadi suka yi kara

Sojojin kasar Yemen sun bada labarin cilla wasu karin makamai masu linzami kan HKI a tsiyar daren jiya, wanda yasa jiniyoyin girgadi suka yi kara a birane da dama daga ciki har da birnin Tel’aviv ko Yafa babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labaran HKI na fadar haka. Sun kuma kara da cewa an ji karar tashin boma-bomai a jere a tsakiyar kasar.

Labarin ya kara da cewa makami guda ne sojojin yemen suka cilla amma tunda ba san inda zai fado ba, a dole miliyoyin mutane suka ruga zuwa wajejen boya da aka tanadar masu.

Labarin ya kara da cewa makami mai linzamin ya ratsa ta saman garkuwan makamai masu linzamu na HKI amma sun kasa gane shi har ya fada a kan bararsa.

Sanarwan da sojojin kasar Yemen suka bayar, bayan cilla wannan makamai mai linzami, ya ce sun cilla makamin ne don tallafawa Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke wa kissan kiyashin kimani watanni 15 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments