Sojojin Kasar Yamen Sun Maida Martani Ga Hare-Haren Amurka Kan Amurkan Da Kuma HKI

Sojojin kasar Yamen sun bada sanarwan maida martani ga hare-haren jiragen yakin kasar Amurka a kan kasar na baya-bayan nan, kuma zasu ci gaba da

Sojojin kasar Yamen sun bada sanarwan maida martani ga hare-haren jiragen yakin kasar Amurka a kan kasar na baya-bayan nan, kuma zasu ci gaba da kai hare-haren kan wadannan wurare har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza.

Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a yau Laraba . Ya kuma kara da cewa, a wannan karon sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, kan wasu wurare masu muhimmanci a birnin Yaffa (tel’aviv). Haka ma sun cilla wasu makaman kan jirgin yaki mai daukar jiragen sama na Amurka wato USS Harry Truman dake arewacin tekun red Sea.

Kafin haka dai jiragen Amurka wadanda suke tasowa daga jiragin yaki USS Harry Truman sun kai hare-hare kan wurare daban daban a kan kasar ta Yemen.

Tun cikin watan Octoban shekara ta 2023 ne sojojin kasar Yemen suka shiga yaki da kuma HKI da kasashen da suke tallafa mata, saboda tallafa wa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI take masu kissan gilla tun lokacin.

Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan kafa kawance ta tabbar da amincin jiragen kasuwanci na HKI a cikin tekun Red sea amma ta kasa samar da aminci ga jiragen HKI a ko masu zuwa wajenta a tekun har yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments