Majiyar sojojin kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa, wasu mutane dauke da makamai daga kasar Siriya sun yi kokarin shiga kasar inda suka zo wuraren bincike na sojojin kasar na kan iyakar kasar ta kasar Siriya, tare da harba bindiga ta sama.
Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto ‘sashen watsa labarai na Sojojin Lebanon na fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata.
Ya kuma kara da cewa, sojojin kasar ta Lebanon sun maida martani da harbin bindiga ta sama don gargadi, wanda ya tilastawa yan ta’addan komawa cikin kasar ta Siriya.
A ranar lahadin da ta gabata ce, wato 27 ga watan Nuwamban da ya gabata, yan adawa da gwamnatin kasar Siriya masu samun goyon bayan kasashen Turkiyya da wasu kasashen yamma, suka fara yaki da gwamnatin kasar shugaba Bashar Al-Asad, daga yankunan Idlib da kuma Alappo.
Sannan zawa ranar 7 ga watan Decemba, yan tawayen sun kama biranen Aleppo, Hama, Deir ez-Zor, Deraa, da kuma Homs. Sai kuma a ranar 8 ga watan Dedcemba suka shiga birnin Damascus babban birnin kasar, ba tare da fuskantar wata Turjiya ba.
Saboda sojojin kasar ta Siriya sun fice daga birnin, sannan shugaba Bashar Al-Asad ya fice daga kasar bayan ya kasa samun fahintar juna da yan tawayen. Da haka kuma gwamnatinsa ta Fadi.