Sojojin sama na JMI sun sami nasarar kakkabo jiragen yaki na makiyan da aka sawwara, tare da amfani da makami mai suna Majid a cikin atisayen sojojin sama da suke gudanarwa a kudu masu yammacin kasar.
Jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa dai, suna da masu muhimmanci a yakin zamani a halin yanzu, don haka sojojin sama na kasar suka bawa al-amarin muhiommanci.
Banda haka tana da makiya wadanda suke da su a yankin wadanda suek amfani da irin wadannan makamai.
A atisayen dai an sawwara jiragen makiya da dama a sararin samaniya, wadanda suke kokarin fadawa kasar, sannan aka cilla makaman garkuwan sararin samaniya samfurin Majid wadanda suka kakkabosu gaba daya.