Sojojin Isra’ila Suna Ci Gaba Da Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Zirin Gaza

Falasdinawa da dama ne suka yi shahada wasu kuma suka jikkata sakamakon munanan hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da aiwatar da kisan

Falasdinawa da dama ne suka yi shahada wasu kuma suka jikkata sakamakon munanan hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi a Gaza

Rahotonni sun bayyana cewa: Sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 431 a jere, ta hanyar kai hare-hare kan mai uwa da wabi ta sama, da kuma harba makaman roka, a yayin da suke aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula musamman kan mata da kananan yara da kuma tsofaffi, a daidai lokacin da ake cikin wani mummunan yanayi na jin kai sakamakon hare-haren wuce gona da iri da killace yankin na Gaza da suka yi, baya ga tserewar Falasdinawa fiye da kashi 95% na al’ummar yankin.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, jiragen yakin sojojin mamayar sun ci gaba da kai hare-hare da muggan bama-bamai a safiyar yau Talata, kan sassa daban-daban na Zirin Gaza, inda suka din ga tarwatsa gidaje da sansanonin ‘yan gudun hijira da luguden wuta kan tituna, inda suka janyo shahadan Falasdinawa da dama da kuma jikkatan wasu na daban.

Har ila yau, sojojin mamayar sun ci gaba da killace wasu manyan unguwanni a birnin Rafah, tun daga ranar 7 ga watan Mayun da ya gabata, da wasu yankuna na Gaza, baya ga luguden bama-bamai da jiragen sama suke yi kan yankunan tare da harba manyan bindigogi kan yankunan, kamar yadda suke harba bama-bamai kan gidajen mutane a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments