Sojojin Isra’ila Na Kai Hare-Hare Kan Gaza A Matsayin Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta

Falasdinawa da dama ne suke ci gaba da yin shahada sakamakon ci gaba da kai hare-hare kan Zirin Gaza da Yahudawan Sahayoniyya ke yi An

Falasdinawa da dama ne suke ci gaba da yin shahada sakamakon ci gaba da kai hare-hare kan Zirin Gaza da Yahudawan Sahayoniyya ke yi

An kashe fararen hula Falasdinawa da dama, wasu kuma sun jikkata yayin da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren sama a yankin Gaza tun jiya da daddare, wanda hakan keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne.

Majiyoyin lafiya sun ruwaito cewa adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 65 tun jiya da daddare har zuwa wayewar gari a yau Laraba, ciki har da 18 daga birnin Gaza da arewacin yankin Gaza, 40 daga tsakiyar yankin Gaza, da kuma 7 daga Khan Younis.

Majiyoyin yankin sun ruwaito cewa jiragen yakin sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan wani tanti a sansanin ‘yan gudun hijira na Insan da ke gabashin Asibitin Shahidai na Al-Aqsa da ke Deir al-Balah, inda suka kashe Falasdinawa biyar: Islam al-Batrighi, Omar Subhi Rubi, da ‘ya’yansa biyu, Awais da Raseel, da Shaimaa Sami Rubi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted