Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a jiya Lahadi Fira minista Benjamin Netanyahu ya bayar da umarnin a rushe gidajen na Falasdinawa.
Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa wannan shi ne hari irinsa na farko da aka rushe gidaje 100 a lokaci kadan.
Masu bin diddigin abinda yake faruwa suna cewa, da alama HKI tana son shafe sansanin ‘yan hijirar na Jenin ne baki daya.
Kungiyoyin Falasdinawa da su ka hada da Hamas sun yi kira da a takawa HKI akan wannan irin barna da take yi.