Sojojin HKI Sun Kutsa Cikin Yankuna Da Dama A Yamma Da Kogin Jordan

Sojojin HKI sun kutsa cikin yankuna da dama a yankin yamma da kogin Jordan a safiyar yau Asabar, inda suka gamu da turjiya daga dakarun

Sojojin HKI sun kutsa cikin yankuna da dama a yankin yamma da kogin Jordan a safiyar yau Asabar, inda suka gamu da turjiya daga dakarun Falasdinawa wadanda suke kokarinn maida su.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa sojojin yahudawan sun kama dan jirida guda a garin Jaba’a da ke kusa da sansanin yan gudun hijira na Jenin a yayinda suka kai bafalasdine guda ga shahada a yannkin Khalil.

Wasu kafafin yada labarai na sada zumunta wato Internet sun bayyana cewa shahidin shi ne Ibrahin Za’aaqiq, dan shekara 20 a duniya kuma ya taba zaman kaso a hannun yahudawan, amma a safiyar yau Asabar ya yi shahada sanadiyyar albarsan da sojojin yahudawan da suka sami shi a cikin gida.

Labarin ya kammala da cewa Ibrahim bai fi makonni biyu da fita daga gidan yari ba ya hadu da ajalinsa a hannun sojojin yahudawan a safiyar yau.

A Zirin Gaza kuma, a wasu sabbin hare haren da sojojin HKI suka kai da jiragen yaki  a Nusairat sun kashe Falasdinawa akalla 24. Labarin ya kara da  cewa, a gida guda a garin Nusairat sojojin yahudawan sun kasashe mutane 8. Banda haka hare haren sun kai garin Gaza da kuma Jabalia duk a zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments