Sojojin HKI, Daga Jiya Zuwa Yau lahadi Kadai Sun Kashe Falasdinawa 62

Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran

Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashen masu neman abainci ne, a cibiyoyin karban abincin wadanda HKI da Amurka suka kafa.

Kafafen yada labarai daga asbitocin Gaza sun bayyana cewa a jiya Asabar yahudawan sun kashe mutane 38 masu neman abinci. Labarin ya kara da cewa, duk tare da sanarwar da gwamnatin HKI ta bayar na tsagaita wuta a wani bangar na zirin gaza, saboda bawa Falasdinawan dama samun agaji daga wasu wurare amma sojojin HK sun ci gaba da kashe Falasdinawan .

Zuwa ranar jumma’an da ta gabata, sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 105 cikin wadanda suka fito neman abinci kadai. A ranakun laraba da Alhamis da suka gabata, hukumar abinci ta duniya ta bayyana cewa sojojin yahudawan sun ci gaba da kashe Falasdinawa a gaza akan neman aminci, wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Tace tun baya fara wannan shirin bada abinci sojojin HKI sun kashe falasadinwa 1,373 kan karban abinci kadai.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted