Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa da dama daga cikin sojojinsu dake Gaza sun jikkata sanadiyyar harin ‘yan gwagwarmaya.
Majiyar ta ambaci cewa a cikin sa’oi 24 da su ka gabata wasu sojoji biyu sun jikkata.
Wannnan sanarwar dai tana zuwa ne a lokacin da dakarun “ Kassam’ na Hamas su ka bayar da labarin cewa sun yi sojojin mamayar kwanton bauna a yankin ‘al-zanah’dake gabashin Khan-Yunus.
Sau da yawa sojojin mamayar HKI suke boye asarar da suke fuskanta a cikin zirin Gaza,musamman ma dai a yankin Khan-Yunus da suke riya cewa suna mamaye da shi.