Falasdinawa 33 ne suka yi shahada, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a luguden wutar da jiragen saman yakin sojin mamayar Isra’ila suka yi kan Gaza
Rahotonni sun bayyana cewa: Tun daga wayewar garin jiya Litinin jiragen saman yakin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi ta yin luguden wuta kan yankuna da dabana-daban a Zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahadan Falasdinawa 33 tare da jikkatar wasu da dama.
Har ila yau, An tattara gawarwakin shahidai goma sha uku na iyalan gida daya da yawancinsu mata da kananan yara ne da aka kashe a wani farmaki da aka kai kan gidansu a lokacin da suke cikin gidansu a garin Beit Lahiya a daren Lahadi wayewar garin Litinin.
Haka zalika, hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan Gaza bai tsaya nan ba, ta kuma kara da daukan matakan killace al’ummar Gaza ta hanyar hana isar kayan agaji da magunguna gare su, inda ta hana isar da manyan motoci da kayayyaki sama da dubu takwas zuwa yankin arewacin zirin Gaza.