Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila ya ba da umarnin tsananta kai hare-hare kan yankunan yammacin gabar kogin Jordan biyo bayan hare-haren bama-bamai da aka kai a birnin Tel Aviv
Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bada umarnin kai hare-haren wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkaram da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan a jiya Juma’a.
Yanzu kusan wata guda ke nan da Netanyahu ya ba da umarnin tsananta hare-haren kan sansanin ‘yan gudun hijiran na Tulkram, kamar yadda ofishinsa ya bayyana, kwana guda bayan tashin bama-bamai kan motocin bus-bus a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Ofishin fira ministan ya bayyana cewa: Kwanan nan ne Netanyahu ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkaram” inda ya ba da umarnin kara kai hare-haren wuce gona da iri kan yankin.