Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada sanarwan shahadar daya daga cikin masu bada shawara kan harkokin tsaronta bairane a kasar Siriya.
Shafin labarai na Parsnews ya bayyana cewa Shahidin Qudus Behruz Wahidi yay i shahada ne a lokacinda jiragen yakin HKI suka kai farmaki kan garin Dairzoor na kasar Siriya inda yake aiki.
Labarin ya kara da cewa Shahid Wahidi dan garin Karaj a lardin Albus da ke kusa da Tehran ne. Kuma yana da aure da kuma yaro dan shekara 2 a duniya.
Labarin ya kara da cewa da dama daga cikin dakarun Qudus na IRGC suna aikin bada shawara ga sojojin kasar Siriya a fafatawan da suke da kungiyoyin yan ta’adda a kasar Siriya. Kuma je kasar Siriya ne tare da bukatar gwamnatin kasar don kare yankin Asiya ta kudu don tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Tun shekara ta 2014 ne kungiyar Daesha wacce take samun goyon bayan kasashen yamma musamman Amurka take kokarin hargitsa al-amuran tsaro a yankin Asiya ta kudu.