Shugabannin Afirka Ta Kudu, Malaysia Da Colombia Sun Yi Kira Da A Kawo Karshen Laifukan Isra’ila

Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malesiya da kuma Colombia sun bukaci da a hukunta laifukan da Isra’ila ke yi na keta dokokin kasa da

Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malesiya da kuma Colombia sun bukaci da a hukunta laifukan da Isra’ila ke yi na keta dokokin kasa da kasa.

A makalar da suka rubuta a mujalar harkokin waje, shugabannin sun bayyana cewa “Zabin abu ne mai wuyar gaske: ko dai mu yi aiki tare don tilasta dokokin kasa da kasa ko kuma mu yi kasadar rugujewar sa.”

Shugabannin sun kara da cewa “harin da ake kaiwa al’ummar Falasdinu ya yi daidai da ababe marasa dadi da munin tarihin da suka faru a cen baya kan kasashensu”, da suka hada da mulkin mallaka, yaki da ta’addanci da wariyar launin fata.

“Muna iya fitowa daga nahiyoyi daban-daban, amma muna da tabbacin cewa rashin tsawatarwa na da hannu cikin irin wadannan laifuka.

Kasashen uku dai dukansu na daga cikin wadanda suka yi tir da Allah wadai da kisan kare dangin da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza.

Afirka ta Kudu kuma ita ce ta jagoranci shigar da karar Isra’ila a Kotun Duniya ta ICJ, kan laifukan yaki a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments