Nicolas Maduro shugaban kasar Venzuwela yayi tir da barazanar da Washington ke ta nanatawa na yin amfani da karfin soji kan karakas, kuma yayi gargadi game da shirin Amurka na kwace ikon kila da rijiyoyin mai na kasar a hanyar amfani da karfin soji.
Maduro yayi wannan bayanin ne a cikin wata wasika da ya aikewa sakatare janar din hukumar kula da hakon manfetur ta duniya OPEC,
Kasar venuzuwela a hukumance ta bayyanawa hukumar cewa gwamnatin Amurka tana so kwace kula da rijiyoyin manta, mafi girma a duniya, ta hanyar yin amfani da karfin soja akanta da mutane da sauran humumomin kasar,
Haka zalika ya fadi a cikin wasikar cewa zai ci gaba da tsayawa kyam wajen kare arzikin makamashi da kasar ke da shi,kuma ba zai mika wuya ga duk wani bata suna ko barazana ba
Wannan wasika ta zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump yayi barazana a ranar Asabar cewa za’a rufe dukkan sararin samaniyar kasar venuzuwela.