Shugaban Turkiyya Ya Bukaci Hadin Kan Al’ummar Musulmi Waje Kalubalantar ‘Yan Mamaya

Shugaban kasar Turkiyya ya yi kira da a kafa kawancen rundunar kasashen musulmi domin kalubalantar gwamnatin yahudawan sahayoniyya Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya

Shugaban kasar Turkiyya ya yi kira da a kafa kawancen rundunar kasashen musulmi domin kalubalantar gwamnatin yahudawan sahayoniyya

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya ce: Dole ne kasashen musulmi su kulla kawance kan abin da ya kira matsayin karuwar barazanar fadadar mamayar yahudawan sahayoniyya, wanda furucin ya fuskanci suka daga ministan harkokin wajen gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Erdogan ya bayyana haka ne bayan da jami’an Falasdinu da na Turkiyya suka bayyana cewa: Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun harbe wata mace ‘yar asalin Amurka da Turkiya a lokacin da take halartar zanga-zangar nuna rashin amincewa da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na fadada matsugunan yahudawa sahayoniyya ‘yan kaka gida a gabar yammacin kogin Jordan.

A yayin wani taron kungiyar makarantun Musulunci da ke kusa da birnin Istanbul Erdogan ya bayyana cewa: Mataki daya tilo da zai kawo karshen girman kai, cin zarafi da ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila shi ne kafa kawancen kasashen musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments