Shugaban Tinubu Ya Tube Kyara A Matsayin Shugaban Kamfanin NNPC Ya Kuma Sannan Ya Maye Gurbinsa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tube shugaban kamfanin man fetur ta kasa NNPC Mele Kyari, da majalisar gudanarwan kamfanin,

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tube shugaban kamfanin man fetur ta kasa NNPC Mele Kyari, da majalisar gudanarwan kamfanin, ya kuma maye gurbinsa ta da wani.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto kakakin fadar shugaban kasa Bayo Onanuga yana fadar haka a safiyar yau Laraba a wani sakon da ya aka a shafinsa na X.

Onanuga ya ce shugaba Tinubu ya tube shugaban kamfanin na NNPC Mele kyari da majalisar gudanarwan kamfanin ne wada aka nada shi a cikin watan Nuwamban shekara ta 2023.

Sannan ya kara da cewa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Kyari a matsayin shugaban kamfanin na NNPC tun kafin haka, sannan Buhari ya sake nada shi a karo na biyu a shekara ta 2023.

Kakakin fadar shugaban kasa ya maye gurbin Mele ne da Engineer Bashir Bayo Ojulari. Ojulari shi ne sabon shugaban kamfanin, sannan ya nada sabbin yan majalisar gudanarwa 11 a kamfanin. Sannan majalisar ta nada Ahmadu Musa Kida a matsayin mataimakin shugaban kamfanin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments