Shugaba Basshar Asad na kasar Syria wanda ya fitar da sakon ta’aziyyar shahadar Sayyid Hassan Narallah ya baynnan cewa; Shahadar jagororin kungiyar gwgawarmaya bay a raunana ta.
Shugaba Basshar Asad ya bayyana Sayyid Hassan Nasara da cewa; Shahidi ne mai mukami na koli, wanda ya bar wa ‘yan baya tunani na gwagwarmaya da rayuwa a cikin daukaka.
Har ila yau shugaban kasar ta Syria ya ce; Al’ummar Syria ba za su taba mantawa da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah ba saboda yadda ya kasance a tare da su, don haka sunansa zai dawwama a tare da su.
A ranar Juma’a 27 ga watan Satumba ne HKI ya kai hare-hare masu tsanani akan unguwar “Dhahiya” da ya kai ton 85 na bama-bamai, da hakan ya yi sandiyyar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah.
A ranar Asabar din da ta gabata ma dai HKI ta sanar da kashe Sheikh Nabil Kawuk wanda shi ne mataimakin shugaban Majalisar zartarwa ta Hizbullah.
A sanarwar da ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta fitar t ace ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 700,wadanda kuma su ka jikkata sun kai 2000 da 600.