Kamfanin Dillanacin “Mehr” Na Iran Ya nakalto cewa, shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya isa birnin Addis Ababa inda ya sami kyakkyawar tarbar takwaransa na wannan kasa, tare da tawagar da take yi masa rakiya.
Daga cikin masu yi wa shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran din rakiya da akwai shugaban kwamitin kawance a tsakanin majalisun kasashen biyu, Manocheri Muttaki, da kuma wasu ‘yan majalisar.
Tun da fari shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana cewa; kasar Habasha memba ce a cikin kungiyar BRICS, da hakan yake a matsayin wata babbar dama ga Iran ta fuskar bunkasa tattalin arziki da ita.
Kalibaf ya furta hakan ne dai a yau Alhamis a lokacin da yake barin Iran akan hanyarsa ta zuwa Addis Ababa.
Bunkasa alaka da kasashen Afirka yana daga cikin muhimman manufofin jamhuriyar musulunci ta Iran.