Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce Akwai Tabbacin Makomar Kasar Siriya Zata Kyau Na Gaba

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Suna da yakinin makomar Siriya ba za ta kasance kamar yadda masu kulla makirci kan kasar

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Suna da yakinin makomar Siriya ba za ta kasance kamar yadda masu kulla makirci kan kasar suka shirya ba

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar al’umma da ake zalunta.

Shugaban Majalisar Shawarar Musuluncin a cikin jawabinsa ya yi ishara da jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Imam Sayyid Ali Khamenei ya yi game da sabbin abubuwan da suke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya musamman a kasar Siriya, inda ya ce: Suna godiya ga Allah da ya yi musu wannan ni’imar ta samun malamin fikihu na musamman Marigayin Imam Khumeini {yardan Allah Ya Tabbata a gare shi}, kuma suna aiki ne don aiwatar da wasiyyarsa da ya ce: Ku kasance cikin masu goyon bayan jagorancin malaman masanin ilimin fikihu don kada wata cutuwa ta same ku.

Shugaban Majalisar Shawarar ta Musulunci ya ce: Tabbas a fili yake cewa rugujewar gwamnatin Bashar al-Assad na iya haifar da matsala ga bangaren gwagwarmaya, amma bangarorin ‘yan gwagwarmaya musamman kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta nuna cewa ba wai kawai ba ta aminta da wannan sabon yanayi ba ne, za ta ma kara hubbasa ne fiye da baya, kamar yadda aka gani bayan shahadar manyan jagororinsu da matsakaitan shugabanni a Hizbullah, yadda gwagwarmaya ta yi karfi fiye da yadda take a baya, kuma ta tilasta wa gwamnatin yahudawan sahayoniyya karbar sharuddan dakatar da bude wuta a Lebanon.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments