Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Akwai babbar damar bunkasa dangantakar tattalin arziki da kasashen Latin Amurka
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf wanda ya yi tafiye-tafiye tun a ranar Asabar din da ta gabata a ziyarar da ya kai kasashen Latin Amurka da Brazil don halartar taron BRICS karo na 11, ya dawo inda ya iso filin jirgin saman Mehrabad na Tehran da yammacin yau Juma’a, bayan kammala ziyarar tasa, inda ya samu tarba daga jami’an gwamnati da na sojin kasar Iran.
Ziyarar na dauke da nufin fadada huldar tattalin arziki da karfafa hadin gwiwa ta hanyar diflomasiyyar majalisar dokoki, kuma ta hada da ganawa da manyan jami’ai a Venezuela, Cuba, da Brazil.
Shugaban majalisar shawarar ta Musulunci ya yi ishara da hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin kasashen Latin Amurka da kasashen musulmi, yana mai cewa: “Akwai babbar dama ga raya huldar tattalin arziki, musamman a fannin makamashi da kuma sha’awar fannonin ilmi.”