Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya cewa: Dole ne a kawo karshen ayyukan dabbancin ‘yan sahayoniyya kan Falasdinawa
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci na kasar Iran, Muhammad Baqir Qalibaf, ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Musulmi da su yi watsi da kawaici saboda harkokin diflomasiyya domin kare mutuncin bil’adama da dukkanin karfinsu a fagen kalubalantar muggan laifukan yahudawan sahayoniyya.
Ajawabin da ya gabatar a yayin zaman farkon ta majalisar shawarar Musulunci a ranar Alhamis din nan, Qalibaf ya ce, idanun duniya sun karkata a kan abin da ke faruwa a birnin Rafah, kuma mutanen da ba su ji ba ba su gani ba suna ci gaba da fuskantar hare-haren wuce gona da iri daga muggan halittu ‘yan sahayoniyya, sun kona sansanonin ‘yan gudun hijira, inda yara da mata da kuma tsofaffi suke mutuwa a birnin na Rafah lamarin da ke kona zukatan al’ummun duniya kuma hakuri da juriyarsu sun kare.