Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata.  Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar  Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik.

A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan dangantaka mai tsawo da ke tsakanin Iran da Pakisatan, da kuma bukatar a kara zurfafata.

Sharif a nasa bangaren ya bayyana cewa nan ba da dadewa waministan harkokin wajen kasar Mohammad Ishak Dar zai ziyarci Tehran inda ake saran zai rattaba hannu kan yarjeniyoyi na bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, daga ciki har da batun kammala aikin shimfida bututun gas  daga kasar Iran zuwa Pakistan. Da kuma harkokin sadarwa.

A cikin wannan shekarar ne dai kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjeniyar bunkasa kasuwanci ta dalar Amurka billion 10 a tsakaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments