Shugaban Kungiyar Kwadago Na Kasar Tunisiya Mai karfin Tasiri Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa

Babban magatakardar kungiyar kwadago ta kasar Tunisiya Nuruddin al-Dhabubi ya sauka daga mukaminsa ba tare da bayyana dalilin yin hakan ba. Mai Magana da yawun

Babban magatakardar kungiyar kwadago ta kasar Tunisiya Nuruddin al-Dhabubi ya sauka daga mukaminsa ba tare da bayyana dalilin yin hakan ba.

Mai Magana da yawun kungiyar ta kwadago ta kasar Tunisiyas Sami al-Dhahri ya ce, A jiya Talata ne al-Dhubabi ya gabatar da takardar ajiye aikin nasa, ba tare da cikakken bayani akan dalilinsa na yin hakan ba.

Sai dai kuma ya ce, a bisa doka ba a amince da irin wannan ajiye aikin, sai an kira wanda ya yi hakan a cikin kwanaki 15 da kokarin shawo kansa ya janye matakin da ya dauka.

Dhahiri ya kuma bayyana cewa ba da jimawa ba za a yi taron kwamitocin da suke a karkashin kungiyar domin tattauna abinda ya kamata a yi. Kakakin kungiyar kwagadon ta kasar Tunisiya ya kore cewa mataimakin  babban magatakardar kungiyar tasu, Anwar Qudur, shi ma ya ajiye aikinsa.

Rahotannin sun ambaci cewa ajiye aikin na Dhubabi ba zai rasa alaka da sabanin da ake da shi ba a cikin kungiyar akan yadda za a shirya babban taron 2026.

Ita dai kungiyar kwadago ta kasar Tunisiya tana da tasiri mai girma a harkokin rayuwar al’ummar kasar. A shekarun baya ta taka rawa wajen jagorantar sauye-sauye na siyasa da ma kawar da gwamanti.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted