Faleh Alfayyad Shugaban dakarun Hashdushabi na kasar Iraki ya bayyana cewa dakarun kungiyar suna biyayya ga malaman addini da kuma duk wadanda suka taimaka mata a baya, wajen ganin bayan kungiyar Daesh a kasar. Daga ciki har da JMI.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS na kasa da kasa ya nakalto Fayyad yana fadar haka a lardin diyala a kasar Iraki a yau jumma’a.
Ya kuma kara da cewa dakarun hashdushabia ba zasu taba manta da shahidanta ba daga cikin har da Mahdi Al-muhandis da kuma Shahid kasim Sulamani. Wanda suka bada rayukansu don kafuwar dakarun Hashdu Shabi.
Fayyad y ace, a halin yanzu suna da mayaka wadanda yawansu ya kai dubu 250, kuma a can baya sun sha wahalar samun isassun makamai amma a halin yanzu sun kulla yarjeniya da wasu kamfanoni kera makamai don magance wannan matsalar.
A farkon watan Decemban shekara ta 2020 ne Donal Trump Shugaban Amurka na lokacin sannan wanda zai sake dawowa kan kujerar a cikin kwnaki ma su zuwa, ya bada umurnin a kashe kwamanda rundunar Quds na dakarun IRGC na kasar Iran. Hajja Kasim Sulaimani da kuma Mahdi Al-Muhandis mataimakin rundunar Hashdushabi na kasar ta Iraki.