Shugaban Kenya Ya Janye Kudirin Karin Haraji, Saboda Bore A Kasar

Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya ya janye kudirin Karin haraji da ya janyo mummunar zanga zanga a kasar. Matakin shugaban kasar na zuwa ne

Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya ya janye kudirin Karin haraji da ya janyo mummunar zanga zanga a kasar.

Matakin shugaban kasar na zuwa ne  bayan masu zanga-zanga suka cinna wa majalisar dokokin kasar wuta ranar Talata.

Cikin wani jawabi da ya yi wa kasar, ya ce ya fahimci cewa al’ummar kasar ba sa goyon bayan kudirin, don haka zai jingine shi.

“Na hakura,” in ji mista Ruto, wanda ya ce ba zai sanya hannu kan kudirin dokar ba.

Akalla mutum 23 ne suka mutu a zanga-zangar da aka shafe wunin Talata aka gudanarwa, a cewar kungiyoyin kare hakkin bil adama.

Masu zanga zangar dai  na cewa dokar za ta shafi talakawa ne da yan kasuwa a kasar dake fama da matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kayyaaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments